News
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Ƙirƙirar Rundunar Tsaro Mai Ɗauke Da Makamai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wata doka da zata kafa rundunar tsaro ta jiha domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bayan muhawara mai zafi kan wasu sassa na dokar, majalisar ta amince da tanadi da ke hana duk wani wanda ke cikin jam’iyyar siyasa jagorantar rundunar. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husaini Dala, ya bayyana cewa an yi nazari sosai kan dokar don tabbatar da cewa tana amfani ga kowane ɓangare na jihar.
Dattijo Mai Shekaru 50 Ya Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga, Sun Yi Garkuwa Da Ɗansa Da Iyalansa
Sabuwar dokar ta ba wa jami’an rundunar ikon ɗaukar makamai, cafke masu laifi da kuma hana aikata miyagun ayyuka a faɗin Kano. Dala ya tabbatar da cewa wanda zai jagoranci rundunar dole ne ya kasance ba dan wata jam’iyyar siyasa ba kuma ya fito daga Kano.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
