Connect with us

News

Ƙudirin Sabunta Dokar Harajin VAT Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Zauren Majalisa

Published

on

Majalisar wakilai ta ce gwamnonin na barazanar hana mambobinta takara a 2027 matukar suka goyi bayan dokar haraji ta Tinubu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar.

Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu.

Gwamnatin Tarayya Ta Mallakawa Kanta Bankin Keystone Bayan Hukuncin Kotu

Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya.

Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi.

Yawancin ’yan majalisar sun goyi bayan ƙudirin, inda suka ce hakan zai ƙara wa gwamnati kuɗin shiga tare da bunƙasa tattalin arziƙi ƙasa.

Advertisement

Sai dai wasu, kamar ɗan majalisa Sada Soli, sun nuna damuwa kan wasu sassa da ba a fayyace su ba a ƙudurorin, waɗanda ka iya haifar da matsaloli a nan gaba.

Duk da haka, bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar ta amince da ƙudirin a karatu na biyu ta hanyar kaɗa ƙuri’a.

Mataki na gaba shi ne miƙa ƙudirin ga kwamitocin majalisar domin ƙara yin nazari, tare da gyara matsalolin da ke tattare da ƙudirorin.

Idan aka amince da shi, za a gabatar da shi a karatu na ƙarshe kafin ya zama doka.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending