Connect with us

News

Shuhaba Tinubu Ya Taya El-Rufai Murna Cika Shekaru 65 A Duniya Duk Da Rikicin Siyasa Da’ke Tsakaninsu 

Published

on

1739700350274

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai murnar cika shekaru 65 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin “shugaba, malami, kuma dan siyasa” wanda ya yi shura akan “ƙwazo da hazaka duk da sabanin da suka samu a Siyasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ,Bayo Onanuga ya fitar a ranar Lahadi , Tinubu ya yaba da rawar da El-Rufai ya taka a matsayin wanda ya bada gudunmawa wajen kafa jam’iyyar APC da kuma gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zabuka uku a jere.

Advertisement

 

“Shugaban kasa ya yaba da rawar da Mallam El-Rufai ya taka ta fafutukar da aka yi kafin kafa jam’iyyar APC da kuma gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zabuka uku a jere na 2015, 2019, da 2023,” in ji sanarwar.

Advertisement

 

Tinubu ya kuma yabawa “kokarin da tsohon ministan ya yi na tabbatar da dimokradiyya; kyakkyawar hidimarsa ga al’umma, da nasiha ga matasa masu tasowa.”

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending