Connect with us

News

Duk da Kashe Sama da Tiriliyan 7 a Lantarki, Ƴan Najeriya na Ci gaba da Fama da Matsalar Wuta

Published

on

TCN Ya samar da sabbin taransfoma a Legas don ƙara inganta hasken wutar lantarki a jihar
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Alkaluma na nuni da cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, an kashe aƙalla Naira Tiriliyan 7 da biliyan 200 ta hanyar tallafi da basuka domin inganta wutar lantarki a Najeriya. Sai dai duk da wannan zunzurutun kuɗi, matsalar ƙarancin wuta na ci gaba da addabar al’umma, lamarin da ya sa ana ci gaba da tambayar ingancin irin waɗannan jarin.

Tallafin da gwamnati ke bayarwa

Advertisement

Rahotanni daga The Guardian, ɗaya daga cikin manyan jaridu a Najeriya, sun bayyana cewa duk da yawan kuɗin da aka ware don gyara harkar lantarki, har yanzu ba a samu gamsasshen sakamako ba. Hukumar Kayyade Farashin Wutar Lantarki (NERC) ta tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da fitar da makudan kuɗi ga kamfanonin da ke kula da rarraba lantarki.

An Tsinci Gawar Dalibin Sakandare A Makaranta

A shekara ta 2015, an tallafa wa ɓangaren lantarki da Naira biliyan 225, sannan adadin ya ƙaru zuwa biliyan 302 a 2016 da kuma biliyan 351 a 2017. Wannan tallafi ya ci gaba da ƙaruwa daga naira biliyan 440 a 2018 zuwa biliyan 528 a 2019. A shekarar 2023 an ware naira biliyan 618, yayin da a 2024 da 2025 an ware naira tiriliyan 2 da biliyan 300 da kuma tiriliyan 2 da biliyan 2, bi da bi.

Yadda kuɗaɗen ke tafiya da yadda kwastomomi ke shan wahala

Advertisement

Duk da waɗannan kuɗaɗe da ake kashewa, ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalen wutar lantarki. A halin yanzu, kowanne kwastoma na biyan kusan Naira 208 kan kowanne kilowatt ɗaya da ya amfani da shi.

Bashin da aka ci gaba da ciyowa

Tun bayan sayar da hannayen jarin kamfanonin samar da wuta, sashen lantarki ya ci bashin da ya kai dala biliyan 5 da miliyan 700 daga Bankin Duniya da Bankin Raya Ƙasashen Afirka, tare da karin naira tiriliyan 2 da biliyan 300 daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Advertisement

Matsalar katsewar wuta da gazawar kamfanonin rarraba wuta

A cewar rahotanni, daga shekarar 2013 zuwa yau, an samu katsewar wuta a duk fadin Najeriya sau 160. Duk da haka, kamfanonin da ke rarraba wuta suna ci gaba da samun makudan tallafi daga gwamnati.

A Abuja, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki (AEDC) ya samu sama da naira biliyan 349 a matsayin tallafi, yayin da kamfanonin Eko (EKEDC) da Ikeja (IE) suka samu naira biliyan 269 da 320, bi da bi. Sauran kamfanonin sun hada da PHED (Port Harcourt) da biliyan 178, BEDC (Benin) da biliyan 197, EEDC (Enugu) da biliyan 193.44, JED (Jos) da biliyan 153, KAEDC (Kaduna) da biliyan 173, YEDC (Yola) da biliyan 103, KEDCO (Kano) da biliyan 162.96, da IBEDC (Ibadan) da naira biliyan 294.

Advertisement

Tambayar da ke gaban ‘yan Najeriya

Duk da biliyoyin da aka kashe da kuma tiriliyan da ake ci gaba da warewa, al’ummar Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar rashin wuta. Hakan na ci gaba da jefa tambaya kan ko shin akwai wata mafita ko kuwa har yanzu ana tafiya a kan tso

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *