News
Ina Jin Daɗin Yadda Naburaska Ya Ke Rainawa Ƴan Siyasarmu Hankali — Aisar fagge
A Najeriya, siyasa ta zama wasan kwaikwayo inda ƴan siyasa ke cin karensu ba babbaka. Sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata ya zama ruwan dare, kuma ana yin hakan ne kawai don biyan buƙata, ba tare da wata ƙwaƙƙwarar manufa ba.
Ba sabon abu ba ne ganin manyan ƴan siyasa su na ficewa daga jam’iyya mara mulki a jiha ko ƙasa zuwa jam’iyya mai mulki da zarar sun fahimci ba za su samu abin da suke so ba.
A gaskiya, babu wani ɗan siyasa a Najeriya da bai taɓa canza jam’iyya ba – har ma akwai waɗanda suka yi hakan fiye da sau biyar. Wannan ya nuna cewa siyasar Najeriya ba ta dogara da akida ko manufa mai ƙarfi, sai dai muradin kowa ya cimma burinsa.
A cikin irin wannan yanayi, mutane irin su Naburaska su ka koyi dabarar raina wa ƴan siyasa hankali. Amma abin takaici shi ne yadda talakawa ke ci gaba da shan wahala. Masu mulki ba sa kula da buƙatun waɗanda suka wahala wajen yaƙin neman zaɓensu.
Maimakon su samar da ayyukan yi da ingantaccen rayuwa ga matasa, sai ka ga suna raba manyan motoci da tarin kuɗaɗe ga ƴan fim da comedians – suna fifita masu tasiri a kafafen sada zumunta fiye da wanda suka zuba jini wajen ganin sun kai ga mulki.
Duk da haka, idan aka buƙaci a dakatar da wannan ɗabi’a, sai kaga wasu na kare su da hujjoji marasa tushe – wai don ubangidansu ne ke aikata hakan.
A wasu lokutan ma, su ne ke korafin cewa wani ɗan siyasa ya watsar da jam’iyyar da ta kawo shi.
A ƙarshe, ya kamata mu fahimci cewa siyasar Najeriya tamkar wasan kwaikwayo ce, kuma talaka ne ke shan wahala. Matuƙar ba a samu sauyi da tsaftace al’adar sauya sheka ba tare da ƙwaƙƙwarar hujja ba, to mun yi sallama da siyasar manufahar abada.
