Connect with us

News

Farashin Kayan Abinci Ya Fadi da Kashi 40% a Kano, Cewar Shugaban Kasuwa

Published

on

kasuwa
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Farashin kayan abinci masu mahimmanci kamar shinkafa, fulawa, madara, wake, da spaghetti ya ragu da sama da kashi 40% a Kano, sakamakon matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.

Shugaban Kasuwar Singer, Alhaji Junaidu Zakari, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin. Ya bayyana cewa sassaucin da gwamnati ta bayar ga ‘yan kasuwa ya ba su damar shigo da kayayyaki kamar shinkafa, mai, da spaghetti, wanda hakan ya haifar da saukin farashi a Kano.

Ina Jin Daɗin Yadda Naburaska Ya Ke Rainawa Ƴan Siyasarmu Hankali — Aisar fagge 

“Ba shakka, wannan ci gaba ya samu ne sakamakon kokarin da gwamnatin tarayya ta yi tare da hadin gwiwar ‘yan kasuwa da suka bi dokokin shigo da wadannan kayayyaki. Wannan ne ya sa kasuwanni suka cika da kaya, lamarin da ya haifar da ragin fiye da kashi 40% na farashin su,” in ji shi.

Advertisement

Zakari ya bayyana cewa cire haraji daga sama da nau’ikan kaya 43, tare da isowar sabbin shinkafa da ake sayarwa kan Naira 40,000, ya taimaka wajen habaka wadatar kaya a kasuwa.

A cewarsa, shinkafa da ake sayar da ita kan N120,000 a baya yanzu ta fadi kasa da N80,000, yayin da spaghetti da ke kan N20,000 yanzu ake sayar da shi kan N14,000. Haka nan, fulawa da ake sayar da ita kan N90,000 yanzu ta koma kusan N70,000, sai kuma mai na lita 50 wanda ya ragu daga kusan N100,000 zuwa N70,000.

Sai dai ya ce farashin sukari bai ragu ba kamar sauran kayayyaki, amma suna tattaunawa da kamfanonin Dangote da BUA domin ganin an samu sauki.

 

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *