Connect with us

News

Martanin ‘Yan Mazaɓar Tarauni Ga Yarima: “Mu Ba Dawakai Ba Ne Da Za Ka Ba Mu Dawa”

Published

on

yarima

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani gagarumin cece-kuce ya ɓarke a ƙaramar hukumar Tarauni, jihar Kano, bayan da ɗan majalisar dokokin jihar, Mukhtar Yarima, ya raba dawa da gyero a matsayin tallafin azumin Ramadan ga al’ummar mazaɓarsa.

Advertisement

Tallafin dai ya jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta, inda mazauna yankin suka nuna rashin jin daɗinsu, suna bayyana cewa ba dawakai ba ne da za a ba su dawa da gyero.

RAMADAN: Kada Ku Yi Amfani da Gurbatattun Kaya Wajen Bada Sadaka  – Babban Limamin Jami’a

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, wani matashi mai suna Abba Wrecca ya bayyana yadda aka ga mai gadi yana dukan jama’a da bulala domin gyara layi na masu karɓar tallafin.

Advertisement

“Wannan shi ne tallafin Ramadan na ɗan majalisar Tarauni kuma surukin Rabi’u Kwankwaso. Hatsin dawa da gyero ake raba wa mutane a 2025,” in ji Wrecca.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa, a yayin da takwarorinsa ‘yan majalisa ke rabon motocin hawa, filaye da kayayyaki, Yarima ya gwammace ya raba dawa.

Advertisement

Wani matashi ya bayyana a bidiyo yana cewa:

“Na rantse da Allah uwata ba za ta ci wannan dawa ba da azumin Ramadan.”

Advertisement

Sai dai wasu magoya bayan ɗan majalisar sun kare shi, suna cewa ya raba shinkafa da wake a matsayin tallafi ga al’umma, amma hatsin dawa da gyero na ƙarin tallafi ne ga talakawa.

Al’ummar Tarauni dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, yayin da suke bukatar wakilinsu ya inganta tallafin da yake bai wa jama’a.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending