News
Mutum 1,010 Sun Mutu Sakamakon Hare-hare A Watan Fabrairu – Rahoto
Aƙalla mutum 1,010 ne suka mutu a faɗin Nijeriya sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da na jami’an tsaro a watan Fabrairu, kamar yadda rahoton kamfanin Beacon Security and Intelligence ya bayyana.
Rahoton ya nuna cewa an samu raguwar sace mutane daga 1,101 a watan Janairu zuwa 955 a Fabrairu, amma adadin mutanen da aka kashe ya ƙaru daga 991 zuwa 1,010.
Dalilin Da Ya Sa Aka Hana Gwamna Fubara Shiga Majalisar Dokokin Rivers
Daga ranar 1 zuwa 28 ga watan Fabrairu, an samu hare-hare da tashin hankali har 716, waɗanda suka haddasa satar mutane 955.
Binciken ya kuma nuna cewa mutum 592 daga cikin waɗanda suka mutu fararen hula ne, inda ‘yan bindiga suka fi kai mafi yawan hare-hare 478, yayin da jami’an tsaro suka haddasa 177.
Jihohin da suka fi fama da hare-haren sun haɗa da Katsina, Kaduna, Neja, Zamfara, Sakkwato, Borno, da Kebbi.
Duk da raguwar hare-haren da kashi 2.19 idan aka kwatanta da Janairu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da zama barazana ga al’umma a Nijeriya.
-
News16 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
