News
Tsananin Zafi Da Bullar Cutar Sankarau: NIMET Ta Bayyana Jihohin Da Suka Fi Fuskantar Hadari
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ta fitar da sabon rahoto da ke nuna cewa wasu jihohin kasar za su fuskanci tsananin zafin rana a kwanaki masu zuwa, lamarin da ka iya kara yawaitar cutar sankarau.
Rahoton ya bayyana cewa jihohi 12, ciki har da Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa da Benue, na daga cikin yankunan da za a fuskanci hauhawar zafin har na tsawon kwanaki uku zuwa hudu. Haka kuma, jihohin Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi, Cross River, Taraba, Adamawa, Filato, Kaduna, Zamfara da Sakkwato na cikin wadanda ke fuskantar barazanar karuwar zafi mai tsanani.
Mazauna Garuruwan Alazawa Da Gazan Sun Gudanar Alkunutu Bisa Matsalolin Da Suka Dabaibaye Yankin
A sakamakon haka, likitoci sun gargadi al’umma da su dauki matakan kariya, musamman gujewa yin ayyuka a cikin rana daga karfe 12 zuwa 3 na yamma. Haka kuma, an shawarci masu azumi da su rage yawan zama a wurare masu cinkoso domin gujewa cututtukan da ake dauka ta iska, musamman sankarau.
Ana bukatar jama’a su kula da lafiyarsu ta hanyar shan isasshen ruwa da kuma kare kansu daga hasken rana mai tsanani.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
