News
Cutar Sanƙarau Ta Kashe Sama Da Mutum 50 Yayin Da Cutar Ta Kama Sama Da Mutum 200 A Arewacin Najeriya
Annobar cutar sanƙarau na ci gaba da barazana ga rayukan jama’a a jihohin Sokoto da Kebbi, inda rahotanni ke nuna cewa fiye da mutum 50 sun rasa rayukansu, yayin da cutar ta kama sama da mutum 200.
A jihar Kebbi, ƙananan hukumomin Aliero, Jega, da Gwandu sun fi fuskantar barazanar cutar, musamman ma a Aliero, inda aka ce sai bayan da cutar ta yi ƙamari ne hukumomi suka farga. A Sokoto kuwa, Tambuwal ce ke fama da cutar, inda gwamnatin jihar ta ce tana ɗaukar matakan gaggawa.
Masana kiwon lafiya sun danganta yawaitar cutar da tsananin zafin da ake fama da shi a yankin. Yayin da hukumomi ke ƙoƙarin dakile yaduwar cutar, al’ummar yankin na cikin fargaba, suna bukatar taimakon gaggawa don hana yawaitar mace-mace.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
