Connect with us

News

Hatsari Biyu Sun Canza Rayuwar Nuraddin, Amma Basu Dakushe Burinsa Ba

Published

on

IMG 20250318 WA0019

 

Nuraddin ya fuskanci manyan jarabawa guda biyu a rayuwar sa—hatsarurruka da suka bar shi da nakasa, amma bai bar hakan ya hana shi ci gaba da rayuwa da kwazon sa ba.

Advertisement

An haifi Nuraddin a shekarar 1991 a karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano. Rayuwar sa ta fara kamar ta kowane yaro mai lafiya, ya kuma fara makarantar firamare da himma.

Bayan kammala firamare a 2003, ya shiga sana’ar injin nika don tallafawa iyayensa.

Advertisement

A nan ne hatsari na farko ya auku—hannunsa ya makale a injin nika, wanda ya tilasta a yanke shi. Duk da haka, bai karaya ba, ya koma sana’ar sayar da fetur a bakin titi, har ya samu damar ci gaba da karatun sakandire.

Tinubu Ya Cutar da Al’ummar Rivers Ta Hanyar Ƙaƙaba Dokar Ta Ɓaci — Atiku

Bayan ya kammala sakandire a 2014, ya samu gurbin karatu a Northwest University, Kano, kuma ya dauki nauyin kansa har ya kai ga bautar kasa a 2019. Lokacin da ya shiga sansanin NYSC, an ba shi damar komawa gida saboda lalurar da ke tare da shi, amma ya nace cewa zai iya yi wa kasa hidima a ko’ina.

Advertisement

Hakan ya kai shi Taraba, inda hatsari na biyu ya faru. A hanyarsu ta zuwa garin Gembu, motarsu ta yi mummunan hadari.

A sakamakon haka, hannunsa na dama ya yanke, kuma idonsa guda daya ya samu matsala mai tsanani. An dauki tsawon lokaci ana jinyar sa, an kuma yi masa aiki don sanya hannun roba. Duk da matsalolin da suka faru, bai tsaya ba—ya cigaba da kokarin inganta rayuwarsa.

Advertisement

A karshe, Nuraddin ya samu aiki a Kano State Polytechnic, daga nan kuma aka tura shi Nigeria Social Insurance Trust Fund (NSITF). Duk da irin jarabawarsa, bai taba barin burinsa ba.

Yanzu haka yana fuskantar wasu kalubale biyu: jinkirin ci gaba da kula da idonsa a Kaduna, da kuma sharadin da asibitin Legas ya gindaya na komawa bayan wata uku don duba hannun roba da aka sanya masa.

Advertisement

Nuraddin ya zama abin koyi na jajircewa, kwazo, da nuna cewa nakasa ba ita ce karshen rayuwa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending