News
Kantoman Ribas Ya Dakatar Da Dukkan Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa

Gwamnatin Jihar Ribas ta dakatar da duk masu riƙe da muƙaman siyasa a faɗin jihar daga aiki nan take.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kantoman jihar, Manjo Janar Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya fitar a daren ranar Laraba.
Sarki Aminu Ado Bayero Ya Janye Hawan Sallah Ƙarama Saboda Dalilin Tsaro
Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya samu ne bisa ga ikon da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa Ibas.
Sarki Aminu Ado Bayero Ya Janye Hawan Sallah Ƙarama Saboda Dalilin Tsaro
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Shugaban Ma’aikata, dukkanin Kwamishinoni, tare da mambobin kwamitoci, hukumomi, da cibiyoyin gwamnati.
Haka kuma, dukkanin Masu Ba da Shawara na Musamman, Mataimaka na Musamman, su ma an dakatar da su.
Sanarwar ta umarci dukkanin waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga Sakatarorin ma’aikatun da suke jagoranta. Idan babu Sakatare, sai miƙa ragamar ga Babban Darakta mafi girma ko Shugaban Harkokin Gudanarwa.
Wannan umarni zai fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025.