Connect with us

News

Hukumar Shari’ah ta Kano Ta Rabauta Da Bohal Mai Darajar Sama Da Naira Miliyan 10 Daga Kungiyar WAMY

Published

on

IMG 20250327 WA0026

Hukumar Shari’ah ta Jihar Kano ta karɓi gudunmawar bohal mai zurfin sama da mita 150 daga kungiyar World Assembly of Muslim Youth (WAMY), wanda ya kai darajar sama da Naira miliyan 10. An ƙaddamar da wannan katafaren bohal yau Alhamis a harabar hukumar.

Da yake jawabi a madadin shugaban hukumar, Sheikh Ali Danabba ya bayyana cewa wannan tallafi wata babbar sadaka ce da za ta taimaka matuka ga ayyukan hukumar. Ya gode wa Allah da kuma kungiyar WAMY bisa wannan gagarumin aiki na sadakatujjariya.

Kantoman Ribas Ya Dakatar Da Dukkan Masu Riƙe Da  Muƙaman Siyasa

Sheikh Danabba ya ce kafin samar da wannan bohal, rashin ruwa na daya daga cikin manyan kalubalen da hukumar ke fuskanta, amma yanzu an samu sauki.

 

Shugaban Hukumar Shari’ah, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya jinjinawa kungiyar WAMY bisa wannan tallafi, yana mai cewa wannan ba shi ne karo na farko da kungiyar ke bayar da gudunmawa ga hukumar ba. Ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyi da su yi koyi da irin wannan aikin alheri don cigaban musulunci da al’umma baki daya.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar WAMY a Najeriya, Hisham Abdussalam, ya ce suna jin daɗin taimakawa hukumar Shari’ah, kuma hakan na daga cikin burinsu na inganta rayuwar musulmi a Najeriya da ma duniya baki daya.

Advertisement

Hukumar Shari’ah ta Jihar Kano, wadda aka kafa a shekarar 2003 ƙarƙashin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, ta fuskanci koma baya a wasu lokuta, amma a yanzu ana sa ran gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta dawo da martabarta tare da tabbatar da ci gabanta.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending