Connect with us

News

Shugaba Tinubu Na Shirin Naɗa Sabon Shugaban Hukumar INEC

Published

on

zabe

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin naɗa sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa zai ƙare a watan Nuwamba 2024.

Wannan yunƙuri ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da masu fashin baki kan yadda zaɓin sabon shugaban zai shafi sahihancin zaɓuɓɓuka masu zuwa, musamman na 2027.

Hukumar Shari’ah ta Kano Ta Rabauta Da Bohal Mai Darajar Sama Da Naira Miliyan 10 Daga Kungiyar WAMY

Wasu majiyoyi sun nuna cewa akwai tsoma bakin wasu manyan ‘yan siyasa daga ciki da wajen fadar Aso Rock, waɗanda ke son ganin an naɗa mutumin da zai dace da tsarin siyasar Tinubu.

Rahoton JARIDAR VANGUARD ya ambato cewa wani tsohon gwamnan wata jiha daga Kudu maso Kudu na jagorantar wannan yunƙuri na naɗa wanda za a iya sarrafawa don shugabantar INEC.

Tun bayan zaɓen 2023, shakku game da sahihancin INEC ya karu, kuma akwai fargabar cewa naɗa shugaban da wasu ‘yan siyasa za su iya juya shi zai ƙara rage amincewa da tsarin zaɓe a ƙasar.

Masu lura da al’amura na nuna damuwa cewa irin wannan naɗi zai iya lalata sahihancin zaɓen ƙasar, wanda ake kokarin ganin an gudanar da shi cikin adalci.

Advertisement

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa dole ne a nemi shawarar Majalisar Kasa (Council of State) kafin naɗa shugaban INEC, sannan sai Majalisar Dattawa ta amince da naɗin. Duk da haka, gwamnatoci da suka gabata sun naɗa masu biyayya ga jam’iyyarsu a muhimman mukamai a hukumar INEC, lamarin da ya tauye cin gashin hukumar.

Masu suka suna gargadi cewa Shugaba Tinubu ya guji maimaita kuskuren da aka yi a baya, inda aka naɗa mutane masu alaka da jam’iyya mai mulki a matsayin shugabannin INEC. A Ghana, an sami sauya shugabancin hukumar zaɓe ba tare da wata matsala ba, wanda ya taimaka wajen ci gaba da tabbatar da sahihancin zaɓuɓɓuka, abin da Najeriya za ta iya koyi da shi.

Adadin masu kada kuri’a a Najeriya yana ƙara raguwa saboda rashin amincewa da hukumar INEC, matsalolin shirya zaɓe, da rikici a ranakun zaɓe. Daga mutane miliyan 39 da suka kada kuri’a a 2003 (69.1%), adadin ya ragu zuwa miliyan 24 kacal a 2023 (26.7%). Idan haka ya ci gaba, dimokuraɗiyya a Najeriya za ta fuskanci ƙarin matsaloli.

Yayin da wa’adin Farfesa Yakubu ke gab da ƙarewa, Shugaba Tinubu na da damar ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya ta hanyar zaɓar wanda ya cancanta, ba tare da sanya siyasa a naɗin ba. Masu fashin baki na jaddada bukatar gyaran dokokin zaɓe da samun shugabanci mai gaskiya da adalci domin dawo da amincewar ‘yan ƙasa kan tsarin zaɓe.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending