News
Titin Jirgin Ƙasa Daga Legas Zuwa Kano Zai Fara Aiki —Hukumar NRC
Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen fara jigilar kaya ta layin dogo mai ƙaramin faɗi tsakanin jihohin Lagos da Kano.
Manajan Daraktan NRC, Kayode Opeifa, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake duba tashar jirgin ƙasa ta Dugbe a Ibadan, Jihar Oyo. Ya ce hukumar tana da ƙwarin gwiwar dawo da jigilar kaya a wannan shiyya tare da ƙaddamar da tashar Dugbe da zarar an fara aiki.
Opeifa ya kuma buƙaci ma’aikatan NRC da su ƙara ƙoƙari wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga, yana mai cewa ƙarin kuɗin da aka samu zai taimaka wajen kyautata albashi da walwalar ma’aikata.
Dangane da matsalar satar kayayyakin jirgin ƙasa, ya nanata cewa NRC ba ta da kayan da suka zama tarkace, yana mai bada umarni ga jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana lalata kayayyakin hukumar.
A yayin ziyarar, Darakta-Janar na Development Agenda for Western Nigeria (DAWN), Seye Oyeleye, ya bayyana cewa suna da shirin haɗa kai da NRC don farfaɗo da jigilar jama’a a yankin kudu maso yamma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
