Connect with us

News

Ba ni da Hannu A Ƙona Majalisar Dokokin Rivers – Shugaban Ma’aikatan Gwamna Fubara

Published

on

e5e685ea 05b9 48e7 a3eb 76d693f04437.jpg

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Rivers, Edison Ehie, ya musanta zargin da ake yi masa na jagorantar ƙona majalisar dokokin jihar a ranar 29 ga Oktoba, 2023.

Ehie ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga tsohon shugaban ma’aikatan jihar, George Nwaeke, wanda ya zarge shi tare da gwamna Siminalayi Fubara da hannu a lamarin.

Advertisement

Gwamnan Kano: A Bayyana Masu Hannu a Kisan ‘Yan Jiharmu a Edo

A wata tattaunawa da tashar Channels, Ehie ya ce ba shi da wata alaka da abin da ya faru.

“Nima kamar kowa, kawai na wayi gari ne a ranar 30 ga watan Oktoba na samu labarin an ƙona majalisar,” in ji shi.

Advertisement

Ehie ya bayyana cewa ya umarci lauyansa da ya maka Nwaeke a kotu bisa zarginsa da ɓata masa suna, yana mai cewa: “Ba zan ce komai a kansa ba, amma ina fata ya shirya gabatar da hujjoji da za su tabbatar da zarginsa.”

 

Advertisement

 

CHANNEL TV

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending