Connect with us

Business

Matatar Ɗangote Ta Saukar Da Farashin Fetur zuwa N865

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta
Spread the love

Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin litar fetur zuwa Naira 865, wanda ke nuna ragin Naira 15 daga tsohon farashin N880. Wannan na zuwa ne a matsayin matakin sassauta farashin mai a ƙasar bayan dawowa da tsarin sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida a farashin naira.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a safiyar Alhamis, hukumomin matatar sun shaida wa dillalai game da sabuwar farashin, wanda ke nuni da sauƙi ga masu saye kai tsaye daga matatar.

Matan Kogi Sun Fito Don Nuna Damuwa Kan Yawaitar Garkuwa da Mutane

A baya-bayan nan, rahotanni daga wasu dillalai sun nuna yiwuwar wannan sauyi, tare da fatan zai taimaka wajen rage tsadar fetur a kasuwannin cikin gida.

Advertisement

Sakataren Ƙungiyar Manyan Dillalan Man Fetur, Mr. Chinese Ukadike, ya bayyana cewa raguwar farashin na da nasaba da matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na fara sayar da ɗanyen mai a farashin naira maimakon dala. Ya ce: “Wannan tsari zai bai wa matatun cikin gida damar sarrafa mai cikin sauƙi kuma a ƙarshe, al’umma za su amfana.”

A ranar Laraba, Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta amince da aiwatar da wannan tsari, wanda aka dakatar da shi a baya. Tun bayan dakatarwar Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) da ta biyo bayan ƙarewar yarjejeniya, farashin mai ya yi tashin gwauron zabi a matatar Ɗangote da sauran gidajen mai na ƙasa.

Lamarin ya tilasta matatar Ɗangote ta koma shigo da ɗanyen mai daga ƙasashen waje, lamarin da ya ƙara ɗora wa al’umma nauyin tsadar fetur. Sai dai da wannan sabon ci gaba, ana sa ran farashin zai ci gaba da sauka a fadin ƙasar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *