Connect with us

News

Babu Doka da Ta Hana Shugaban Majalisa Gabatar da Ƙuduri – Barr Abba Hikima

Published

on

Hikima

Fitaccen lauya Barr. Abba Hikima Fagge ya bayyana cewa babu wata doka da ke hana Shugaban Majalisa ko  mataimakinsa gabatar da ƙuduri a gaban majalisa.

Wannan furuci ya biyo bayan kunshin bayanai da aka fitar dangane da ayyukan mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano na shekarar 2024, wanda ya fallasa rashin gabatar da ƙuduri daga shugabannin majalisar da wasu ‘yan majalisa.

Advertisement

Za A Fuskanci Tsananin Zafin Rana A Kano Da Wasu Jihohin Arewa 17  — NiMet

Kididdigar da aka fitar ta nuna cewa Kakakin Majalisa Jibril Isma’il Falgore da mataimakinsa Muhammad Bello Butu-Butu na daga cikin mambobi bakwai da ba su gabatar da ko da ƙuduri ɗaya ba a shekarar da ta gabata, abin da ya haifar da zargi na zaman “dumama kujera” daga jama’a.

Rahoton, wanda Akawun Majalisa Bashir Idris Diso ya fitar ta hannun wata kafar yada labarai a Kano, ya bayyana hakan ne yayin gabatar da wani shiri da majalisar ta dauki nauyinsa, inda aka nuno cewa mafi yawan mambobin na kasa cika nauyin da aka dora musu.

Advertisement

Sai dai FREEDOM RADIO ta ruwaito cewa a martaninsa, Barr. Abba Hikima yana mai cewa, “Babu wani tanadi a tsarin mulki ko dokar majalisa da ke takaita ko hana shugabannin majalisa gabatar da ƙuduri.” Wannan na iya sauya fahimtar jama’a dangane da rawar da shugabannin ke takawa a majalisa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending