Connect with us

News

Madarasatul Tarbiyatul Aulad Academy Za Ta Yi Bikin Saukar Dalibai 23 A Karo Na Biyu

Published

on

IMG 20250428 WA0032

A ranar Asabar, 3 ga watan Mayu 2025, Madarasatul Tarbiyatul Aulad Academy da ke Sheka Sabuwar Abuja za ta gudanar da bikin saukar karatun Al-Qur’ani mai girma na dalibai 23, karo na biyu, karkashin jagorancin Alhaji Shafi’u Ya’u.

An shirya gudanar da bikin cikin yanayi na farin ciki da annashuwa, inda iyaye, malamai da manyan baki za su hallara domin taya daliban murnar wannan gagarumar nasara. Ana sa ran babban taron zai samu halartar manyan baki da dama, ciki har da uban taro Alhaji Abubakar Musa Zakari (Dagacin Sheka), da uban makaranta, Malam Yusuf Limamun Sheka.

Ɗalibar Najeriya Ta Maka Shugaban Ƙasar Amurka A Kotu 

Daga cikin fitattun bakin da za su halarci bikin akwai:

Alhaji Abdullah Maliya Gidan Kudi

Nura Ahmad Gwaski

Oga Sogira Farm Center

Advertisement

Alhaji Haruna Engineer

Malam Yakubu Director, da sauransu.

Haka kuma, wasu daga cikin manyan bakin na musamman da ake sa ran ganinsu sun hada da:

Alhaji Shafi’u Ya’u (Sarki)

Alhaji Bashir Ali Mai Agogo (Magajin Garin Bawura, Kano)

Hon. Usaman Abubakar Larba

Advertisement

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da sauransu.

Shugabannin kungiyar iyaye da malamai (PTA) na makarantar, karkashin jagorancin Malam Auwal Abubakar, sun nuna cikakken goyon baya ga cigaban makarantar da dalibanta. Malaman makaranta maza da mata, ciki har da Malam Abubakar Ya’u Muhd (Director), Malam Abdullah Yusuf, Malama Zainab Isah (Assistant Director), da Malama Mai’muna Umar Ibrahim (Head Teacher), za su halarci taron cikin cikakken shiri.

Bikin, wanda zai gudana a Sheka/Abuja, layin Malam Sheikh, a gidan Bulon Alhaji Ya’u, zai fara da misalin karfe 9:00 na safe. Za a kaddamar da sabuwar kalandar makarantar a wajen taron, tare da gudanar da addu’o’i na musamman domin fatan alheri ga daliban da suka sauke karatu da kuma cigaban makarantar.

An tanadi tsare-tsare na musamman domin tabbatar da gudanar da taron cikin tsari da zaman lafiya, inda za a rufe shi da addu’o’in albarka ga makarantar da dukkan masu ruwa da tsaki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending