Connect with us

News

’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Daba 33 A Kano

Published

on

Police

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke mutum 33 da ake zargi da aikata ta’addanci a cikin birnin Kano, sakamakon samamen da jami’an rundunar suka gudanar cikin kwanaki biyar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce an kama wadanda ake zargin ne tsakanin 23 zuwa 28 ga Afrilu, 2025, bayan samun bayanan sirri daga jama’a.

Advertisement

Zanga-Zangar Dalibai Ta Tilasta Rufe Kwalejin Adamawa Na Tsawon Mako Daya

Sanarwar ta ce tawagar musamman da CSP Bashir Musa Gwadabe ke jagoranta ta cafke mutanen dauke da makamai masu hadari, miyagun kwayoyi da kayan sata.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa, rundunar za ta ci gaba da gudanar da sintiri da samame don tabbatar da zaman lafiya, tare da karfafa hulda da al’umma domin dakile miyagun ayyuka.

Advertisement

Kwamishinan ya yaba wa hadin kan jama’a tare da bukatar su ci gaba da bai wa ’yan sanda bayanan sirri don taimakawa wajen yaki da laifuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending