Connect with us

News

An Karkatar Da Sama Da Kashi 70 Cikin 100 Na Kudin Rancen Ɗalibai — ICPC

Published

on

images (2)

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta ce sama da kashi 70 cikin 100 na kudin da gwamnatin tarayya ta ware wa rancen ɗalibai an karkatar da su.

Hukumar ta bayyana cewa daga cikin Naira biliyan 100 da aka saki domin ɗalibai a jami’o’i da sauran manyan makarantu, sai dai Naira biliyan 28.8 ne suka isa hannun ɗalibai.

Advertisement

Bankuna Sun Ƙarawa Kwastomominsu Kuɗin Tura Saƙo Zuwa N6

Mai magana da yawun ICPC, Demola Bakare, ya ce binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa Naira biliyan 71.2 ba ta isa ga ɗalibai ba, inda wasu jami’an jami’o’i da makarantu suka karkatar da kudaden.

Ya ce sun gayyaci manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Darakta-Janar na Ofishin Kasafi, Akanta Janar na Ƙasa, jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN), da shugabannin hukumar NELFUND domin bayar da bayani da takardu.

Advertisement

A makon da ya gabata, Darakta-Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya zargi wasu jami’o’i da yunkurin jefa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu cikin matsala ta hanyar karkatar da kudin rancen ɗalibai.

Ya ce aƙalla makarantu 51 ne suka yi cire-cire daga cikin kudaden ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba, inda ake zargin an cire kuɗi tsakanin N3,500 zuwa N30,000 daga hannun ɗalibai.

Advertisement

Bakare ya ce ICPC ta fara bincike tun bayan samun wannan rahoto, kuma za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

A cewar sa, “Daga cikin bayanan da muka samu daga hukumar NELFUND, an bayyana cewa kudin da aka samu gaba ɗaya ya kai Naira biliyan 203.8, ciki har da kudaden da suka fito daga asusun FAAC, EFCC da kuma TETFUND.”

Advertisement

Ya ce zuwa yanzu, makarantu 299 ne suka amfana da kudaden, inda ɗalibai 293,178 suka samu tallafin.

ICPC ta ce akwai manyan bambance-bambance a cikin kudaden da aka raba da na daftarin gwamnati, kuma za ta ci gaba da bincike tare da sanar da al’umma yadda komai ke tafiya. Kashi

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending