News
Saudiyya Ta Sanya Sabbin Matakai Da Tara Masu Tsauri Kan Ƙoƙarin Hajji Ba Tare Da Izini Ba
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar da sabbin ƙa’idoji tare da tsauraran matakan ladabtarwa ga duk wanda ya yi ƙoƙarin shiga Makka ko Madina domin aikin Hajji ba tare da sahalewar hukuma ba.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ranar Litinin, 28 ga Afrilu, 2025, ta bayyana cewa an yanke hukunci da nufin hana masu kutse da kare tsaron mahajjata da lafiyarsu.
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yaba Wa Gwamna Abba Kan Biyan Haƙƙoƙinsu
Tarar Riyal 20,000
Duk wanda aka kama yana yawo ko yana ƙoƙarin shiga Makka ko Madina daga ranar 1 ga Dhul-Qi’dah zuwa 14 ga Dhul-Hijjah ba tare da izini ba, za a ci shi tarar Riyal 20,000.
Tarar Riyal 100,000
Za a ci wannan tara ga:
Duk wanda ya nema wa wani bizar ziyara sannan aka kama shi yana ƙoƙarin shiga Makka da niyyar Hajji
Duk wanda ya ɗauki wani da bizar ziyara domin shiga haramin Makka ko Madina.
Duk wanda ya ba wa waɗanda ke da bizar ziyara matsuguni a Makka ko Madina – ko a gida ne, otel ko wani wuri.
An bayyana cewa za a ninka tarar ne gwargwadon yawan mutanen da aka taimaka musu shiga ba bisa ƙa’ida ba.
Haramta Shiga Saudiyya na Shekaru 10
Duk wanda aka kama yana aikin Hajji ba bisa izini ba, za a hana shi samun biza ko shigowa ƙasar Saudiyya har na tsawon shekaru goma.
Kwace Ababen Hawa
Za a kwace duk abin hawa da aka yi amfani da shi wajen safarar waɗanda suka shige doka – ko na kamfani ne, ko na mutum kai tsaye – bisa umarnin kotu.
Ma’aikatar ta ce wannan mataki na daga cikin shirin kare tsaro da inganta gudanar da aikin Hajji na bana.
Najeriya za ta fara jigilar maniyyata
A Najeriya kuwa, an shirya fara jigilar maniyyatan Hajji daga ranar 9 ga watan Mayu, kamar yadda hukumar NAHCON ta sanar.
Hukumomin sun gargadi jama’a da su guji yin amfani da biza ta ziyara domin kutse aikin Hajji, su kuma tabbata sun samu sahalewa daga hukumomin da suka dace kafin tunkarar kasa mai tsarki.
