News
Kungiyoyin Farar Hula 107 Sun Goyi Bayan Dakatar Da Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye A Kafafen Yada Labarai A Kano

Kungiyoyi 107 na farar hula da ke jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu ga matakin da shugabannin kafafen yada labarai suka dauka na dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a gidajen rediyo.
A cewar kungiyoyin, wannan mataki ya zama dole ne sakamakon yadda shirye-shiryen suka rikide zuwa dandamali na cin zarafi, zarge-zarge marasa tushe da kuma kalaman da ke haddasa rikici a tsakanin al’umma.
UTME 2025: Dalibai 379,997 Ne Za Su Sake Zama Jarabawar JAMB
Shugabannin Media Executive Forum, wato kungiyar shugabannin kafafen watsa labarai a Kano, sun sanar da dakatar da shirye-shiryen siyasar ne domin dakile yadda ake amfani da su wajen tayar da zaune tsaye a tsakanin ’yan siyasa da mabiyansu.
A wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar ranar Talata a Kano, sun ce, “Mun yaba da jarumtar da kungiyar Media Executive Forum ta nuna wajen dakatar da shirye-shiryen siyasa da suka kauce wa hanyar da ta dace da aikin jarida da bin ka’idojin watsa labarai.”
Sun kara da cewa duk da cewa ’yancin fadar albarkacin baki yana da muhimmanci a tsarin dimokuradiyya, ya kamata a rika amfani da shi cikin gaskiya da ladabi tare da kauce wa kalaman da ke haddasa rikici.
“Idan kafafen yada labarai suka zama hanyar yada batanci da rarraba kawuna, to sun kauce daga manufarsu na wayar da kai da karfafa zaman lafiya,” in ji sanarwar.
Kungiyoyin sun kuma bukaci sauran gidajen rediyo da su sake nazarin manufofinsu domin kauce wa zama hanyoyi na yada siyasar karya da kiyayya, tare da kira ga Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Kasa (NBC), da Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki da su sa ido tare da taimaka wa wajen horar da ma’aikatan kafafen yada labarai.
Sun ce wajibi ne a tabbatar da cewa kafafen watsa labarai na taka rawar gani wajen Samar da zaman lafiya, ba su zama makamin siyasa ba.
Sanarwar ta zo ne da sa hannun Hassan Ibrahim Gama da Mustapha Muhammad Chiroma, tare da goyon bayan kungiyoyi 107 da ke aiki a fannonin ci gaban al’umma, kare hakkin mata da yara, ilimi, lafiya da zaman lafiya a jihar Kano.
