News
Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin ISWAP A Marte

Akalla sojoji 20 ne ba a san inda suke ba bayan wani mummunan hari da mayaƙan ISWAP suka kai wa sansanin sojoji da ke Marte a Jihar Borno da safiyar Litinin.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kutsa cikin sansanin inda suka kashe sojoji huɗu tare da sace makamai.
An Kama Mutum Mai Shekaru 47 Bisa Zargin Cin Zarafin ‘Yar Matarsa Mai Shekaru Biyu A Gombe
Wani jami’in tsaro da ke aiki a yankin ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu ba a san halin da waɗanda suka ɓacen suke ciki ba.
“Yanzu haka muna neman sojoji kimanin 20 da ba mu da labarinsu tun bayan faruwar harin. Muna fatan suna raye,” in ji shi.
Sakamakon harin, daruruwan mazauna Marte sun tsere zuwa garin Dikwa domin tsira da rayukansu.
Wata majiya ta ce mayaƙan ISWAP har yanzu suna riƙe da sansanin, kuma ta bukaci gwamnati da ta tura ƙarin jami’an tsaro don dawo da doka da oda.
“Ya kamata a ɗauki matakin gaggawa kafin lamarin ya kazanta,” in ji majiyar.