News
Yadda Wasu Ke Yunkurin Sayar Da Filin Makarantar ’Yan Mata A Kano

Al’ummar yankin Bechi da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano sun koka kan yunkurin wasu mutane da ba a san ko su waye ba da suke ƙoƙarin mallakar filin da aka ware domin gina makarantar sakandaren ’yan mata a yankin.
Al’ummar sun ce filin na makarantar an ware shi ne tun shekarar 2014 a zamanin mulkin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, domin rage cunkoson da ake fama da shi a makarantar firamare, inda ake amfani da lokaci ɗaya domin koyar da ’yan firamare da na sakandare.
Cikin wata sanarwa da Kwamitin Cigaban Al’ummar Bechi da Kewaye (Bechi Community Development Association) ya fitar, ya bayyana cewa Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta amince da gina makarantar sakandaren ’yan mata a yankin, kuma har an fara gina aji guda.
Sai dai daga baya dan kwangilar da ke aikin ya fice da kayan aikin ba tare da wani bayani ba, lamarin da ya bar aikin a kasa.
Kwamitin ya ce hakan ya bai wa wasu dama suka shiga filin da nufin yanka shi domin siyar da wuraren a matsayin filotai ga jama’a.
Shugaban kwamitin SBMC na makarantar, Comrade Adamu Bechi, ya roki Gwamnatin Jihar Kano da ta gudanar da bincike kan yadda aikin gina makarantar ya tsaya cak, tare da hana shirin sayar da filin da aka tanada don ci gaban ilimin ’ya’ya mata.
Ya ce “Makarantar ce kawai mata ke da ita a wannan yankin da kewaye, kuma duk dakatar da aikin ci gabanta na nufin hana dubban yara mata damar samun ilimi.”
A ƙarshe, al’ummar Bechi sun roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya shigo cikin lamarin da gaggawa, domin ceto makomar ilimin ’ya’ya mata a yankin da ma makwabtansu da ke cin gajiyar makarantar.