News
Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Daurin Shekara Guda Da Bulala 60 A Kano
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Ahmad Sa’id Dandinshe hukuncin daurin shekara guda tare da bulala 60 bayan samunsa da laifin satar rago a unguwar Dabai da ke karamar hukumar Gwale.
An gurfanar da Dandinshe a gaban kotu bisa zargin kutse cikin wani gida da satar ragon da mamallakinsa ya tanada don yankan layya a lokacin Babbar Sallah.
Yadda Wasu Ke Yunkurin Sayar Da Filin Makarantar ’Yan Mata A Kano
A gaban kotu, Dandinshe ya amsa laifinsa, lamarin da ya sa lauyan gwamnati ya bukaci a hukunta shi bisa tanadin dokar Shari’a ta jihar Kano.
Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar Naira 15,000 tare da bulala 30 saboda kutse. Sai kuma wani hukunci makamancin haka na watanni shida da bulala 30 saboda laifin sata.
An zartar da bulalar a harabar kotun nan take, wanda hakan ke nufin Dandinshe zai shafe shekara guda a gidan yari idan bai biya tarar ba, kuma ya sha bulala 60.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
