News
Ɓangaren Shari’ar Najeriya Cike Ya Ke da Baragurbin Alƙalai Masu Cin Hanci —El-Rufai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana damuwarsa kan yadda ɓangaren shari’a a Najeriya ke ci gaba da faɗawa cikin halin tabarbarewa sakamakon yawaitar alƙalai da ya bayyana a matsayin “baragurbi” waɗanda suka duƙufa wajen karɓar cin hanci da yanke hukunci bisa son rai.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taron makon shari’a da Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta shirya a garin Bwari, babban birnin tarayya Abuja.
IPAC Ta Ce Dakatar Da Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye Hanya Ce Ta Wanzar Da Daidaito A Kano
Ya ce, “Jama’a sun gaji da yadda shari’a ke tafiya a Najeriya. Mutane sun daina sa rai daga kotu saboda yadda ake jinkirta shari’u da kuma yadda alƙalai ke yanke hukunci bisa son rai da ƙalilan da ke da ƙarfin aljihu.”
El-Rufai, wanda shima lauya ne, ya bayyana cewar cin hanci da rashawa ya yi katutu a tsakanin manyan alƙalai, yana mai cewa wannan matsala na kawo cikas ga zaman lafiya da cigaban ƙasa.
“Shari’a a Najeriya ta koma ta masu kuɗi. Talaka ba shi da wurin tsayawa, domin babu yadda zai iya biya don samun adalci. Wannan ya sa tsarin shari’a ke ƙara dusashewa a idon talakawa,” inji shi.
Tsohon gwamnan ya kuma nuna rashin amincewarsa da ayyana dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, yana mai cewa wannan mataki na iya zama ƙofa da za a riƙa take doka da bin hanya marar tsari.
Ya ja kunnen Ƙungiyar Lauyoyi da su tsananta lura da ayyukan mambobinta da kuma sanya idanu kan yadda alƙalai ke tafiyar da shari’u a kotuna. A cewarsa, “Ba za mu riƙa kiran a gudanar da sahihin zaɓe a ƙasa ba, alhali wasu alƙalai na can na cukuikuye shari’ar zaɓe bisa son rai da amfani da mulki ba bisa doka ba.”
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da Ƙungiyar Lauyoyi za ta tsaya kan gaskiya wajen gyara ɓangaren shari’a domin dawo da martabar kotuna a idon al’umma.
