News
MATSALAR TSARO A NAJERIYA: Akalla Mutune 590 Ne Suka Rasa Rayukansu Yayin Da Aka Sace 192 A Watan Afrilu – Rahoto
Akalla mutane 590 ne suka rasa rayukansu a fadin Najeriya a watan Afrilu kadai, yayin da aka sace wasu 192, a wani yanayi na ci gaba da tabarbarewar tsaro da ke kara kamari a kasar.
Rahoton wata kafa mai zaman kanta ta. a harkar tsaro, HumAngle Security Tracker, ya bayyana cewa an samu aƙalla abubuwan da suka shafi rashin tsaro 201 a watan Afrilu, wanda hakan ya sa watan ya zama mafi muni cikin shekarar 2025.
Farfesa Gwarzo Ya Yaba Wa Shugaban Jami’ar Nile Kan Inganta Ilimi Da Bincike
Rahoton ya ce a kowace rana, ana kashe mutane 20, yayin da ake sace mutum 7 a kullum a faɗin Najeriya.
Yankin Arewa ta Tsakiya shi ne yafi fuskantar illar rashin tsaro, inda aka samu hare-hare 50 da suka yi sanadin mutuwar mutane 233.
Jihar Benue ce ta fi kashe-kashe da adadin mutane 99 da aka kashe, sai jihar Filato da aka kashe mutane 97. Rahotanni sun danganta hakan da hare-haren da ake kai wa ƙauyuka da kuma rikicin makiyaya da manoma.
A cewar WikkiTimes, jihar Filato na fama da rikicin ƙabilanci yayin da jihar Benue ke fama da sabani tsakanin al’ummomin karkara da makiyaya.
A yankin Arewa maso Yamma, an samu hare-hare 47 da suka yi sanadin mutuwar mutane 130. Jihar Zamfara ce ta fi fama da sace mutane, inda aka sace mutum 75 a cikin watan Afrilu kadai. A Katsina kuwa, an sace mutum 64.
A Arewa maso Gabas kuwa, mutane 129 ne suka mutu a cikin hare-hare 37 da aka kai, musamman a jihar Borno, inda kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kai munanan hare-hare.
A fadin yankin Arewa, mutane 446 ne aka kashe a cikin hare-hare 113 da suka shafi fararen hula kai tsaye. Wasu daga cikin hare-haren sun hada da na ‘yan bindiga, masu tayar da kayar baya, da kuma ‘yan fashi da makami da ke addabar al’umma a karkara da kan manyan hanyoyi.
Rahoton ya kuma ce harin bama-bamai da na nesa sun yi sanadin mutuwar mutane 42 a lokuta 8.
Ko da yake akwai hare-hare a Kudancin Najeriya, su ba su da tsanani irin na Arewacin kasar. A jihar Legas, duk da yawan tashe-tashen hankula, ba a samu yawan mace-mace ba. Yankin Kudu maso Kudu ya rasa mutane 29, yayin da Kudu maso Gabas ya rasa mutane 14.
Yayin da lamarin ke kara dagulewa musamman a yankunan Arewa, masana sun ce hakan na barazana ga noma, karatu da rayuwar al’umma a karkara. Yawan sace mutane da kashe-kashe na kara jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali.
Dr. Kabiru Adamu, masani a fannin tsaro kuma Shugaban Beacon Consulting, ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga gazawar gwamnati, rashin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kuma rashin niyyar siyasa wajen magance matsalar.
Ya ce, “Kungiyoyin ta’addanci da na laifi suna cin karensu babu babbaka a karkara saboda gazawar jami’an tsaro, rashin kayan aiki da kuma tsoma bakin yan siyasa.”
Ya kuma jaddada cewa, “Sai an samu hadin gwiwa da amfani da bayanan sirri kafin a iya dakile wannan matsalar.”
