Connect with us

News

Kaɗan Daga Cikin Jawabin Da Shugaba Tinubu Ya Yi Kan Cikarsa Shekaru 2 A Mulki

Published

on

Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun haifar da manyan sauyi wajen farfaɗo da tattalin arziki, inganta rayuwar al’umma da kuma gyaran tubalin ci gaban ƙasa.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a ranar Laraba, yayin bikin cikar gwamnatin sa shekaru biyu da hawansa kan karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Naira Biliyan 16 Ga Tsofaffin Kansiloli Da Manyan Ma’aikata

Ya ce gwamnatin sa ta rungumi tsauraran matakai ne domin fidda ƙasar daga halin kunci da ta tsinci kanta, tare da fatan gina ingantacciyar makoma ga kowane ɗan ƙasa.

> “Mun aza harsashin sabuwar Najeriya da ke buɗe ƙofa ga tattalin arziki mai ƙarfi, da damar zuba jari, da walwalar ‘yan ƙasa,” in ji Tinubu.

Advertisement

Raguwar Tsadar Rayuwa da Gina Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa na kokarin saukaka wa ‘yan ƙasa ta fuskar tsadar rayuwa da sauye-sauyen tsarin tattalin arziki. Ya ce an ɗauki matakan da za su janyo masu zuba jari daga cikin gida da waje, ta hanyar gina kyakkyawan tsari na kasuwanci da fasalin haraji.

Advertisement

Ya gode wa ‘yan Najeriya bisa juriyar da suka yi, duk da ƙalubalen da aka fuskanta bayan cire tallafin man fetur da wasu sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar.

Tsaro: Bunkasa Huldar Jami’an Tsaro da Ƙarfafa Bayanai

Advertisement

A bangaren tsaro, shugaban ya bayyana cewa gwamnatin sa ta dukufa wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya ce an samu ci gaba ta fuskar haɗin guiwar jami’an tsaro da kuma tsarin tattara bayanai domin dakile hare-hare da aikata laifuka.

> “Tun daga ranar da na karɓi mulki, burinmu shi ne kare rayuwar ‘yan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa,” in ji Tinubu.

Advertisement

Aikin Noma da Farashi Kayan Abinci

Dangane da ɓangaren noma, Tinubu ya ce gwamnati ta sanya wannan fanni a gaba, inda ta samar da tallafi da kayayyakin aiki ga manoma. A cewarsa, hakan na daga cikin dalilan da ya janyo raguwar farashin abinci a kasuwanni.

Advertisement

 

Kiwon Lafiya: Ci gaban Cibiyoyi da Tallafin Haihuwa

Advertisement

A fannin lafiya kuwa, Tinubu ya ce gwamnatin sa ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya sama da 1,000 a matakin farko, tare da ci gaba da aikin gyaran wasu 5,500 a fadin ƙasar. Har ila yau, ya ce an kafa sabbin cibiyoyin kula da cutar daji guda 6, inda 3 daga cikinsu aka kammala aikin su.

Ya kuma bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin kiwon lafiya na shugaban ƙasa, mata fiye da 4,000 ne suka amfana da tiyatar haihuwa kyauta a sassa daban-daban na ƙasar.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya kammala da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba, da nufin tabbatar da Najeriya mai ɗorewa da walwala ga kowa da kowa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending