Connect with us

News

Gaskiya Da Rikon Amana Da Kuma Tsoron Allah Ne Mafita – Inji Limamin Gajuna

Published

on

Limamin sabon Masallacin Juma’a da aka gina a garin Gajuna, cikin Mazabar Ruwan Bago a Karamar Hukumar Rogo, Malam Ibrahim Inyass, ya jaddada bukatar rikon amana da biyayya ga shugabanni tare da kauce wa sukar su da ba gaira ba dalili.

Limamin ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ya yi da wakilinmu jim kadan bayan kaddamar da sabon masallacin.

Advertisement

Dr. Joseph Kigbu Ya Gina Dakunan Karatu Kyauta Don Taimaka Wa Ilimin Yara A Lafia

Ya ce: “Duniya tana cikin wani hali na fitina, kuma mafita tana hannunmu idan muka rungumi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW), tare da rikon gaskiya da taimakon juna.”

Malam Inyass ya kuma bayyana gina masallacin a matsayin wata dama ta kusanci Allah da ƙarfafa zumunci tsakanin al’umma, musamman a wannan lokaci da ake fama da kalubalen rayuwa daban-daban.

Advertisement

A nasa jawabin,Hakimin Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Garba Muhammad Bello Dan Isan Karaye, ya bayyana masallacin a matsayin wata muhimmiyar hanya ta farfado da al’adun ibada da raya kalmar Allah.

Ya jinjinawa kokarin shugaban karamar hukumar, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na alkhairi su ne ginshikin cigaban al’umma.

Advertisement

Taron kaddamarwar ya samu halartar manyan baki ciki har da Shugaban Kansiloli, masu ba da shawara na musamman, dagatai, masu unguwanni da sauran shugabannin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending