Connect with us

News

Dr. Joseph Kigbu Ya Gina Dakunan Karatu Kyauta Don Taimaka Wa Ilimin Yara A Lafia

Published

on

Ambaliyar RuwaZulum Ya Rufe Ɗauƙacin Makarantun Firamare Da Ke Jihar Nan Take

Sabon Kwamishinan Hukumar Ƙididdigar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dr. Joseph Kigbu, ya gina dakunan karatu guda uku da ofishi ɗaya ga makarantar firamare ta RCM da ke Barraki Abdullahi a karamar hukumar Lafia, Jihar Nasarawa.

Aikin, wanda ya kai kuɗi Naira miliyan 55, an kammala shi ne don inganta karatu da ƙarfafa sha’awar ilimi ga yara, musamman masu tasowa a ƙauyuka.

Advertisement

Rabin Al’ummar Duniya Sun Fuskanci Matsanancin Zafi Saboda Sauyin Yanayi — RAHOTO 

Da yake jawabi a wajen mika aikin ga wakilan Gwamnatin Jihar Nasarawa a ranar Juma’a, Dr. Kigbu ya ce wannan aikin na daga cikin rawar da ya ɗauka na mayar da alheri ga al’ummar da suka taimaka masa.

> “Wannan makarantar na daga cikin wacce na halarta a baya. Allah ya ɗaga ni, yanzu lokaci ne na mayar da alheri. Ina so yaran mu su koyi karatu cikin walwala da wutar lantarki, fanka da kujeru masu kyau ba tare da sai sun je birni ba,” in ji shi.

Advertisement

Dr. Kigbu, wanda ya wakilci mazaɓar Lafia/Obi a Majalisar Wakilai daga 2011 zuwa 2015, ya ce tallafa wa al’umma ba sabon abu ba ne a wajensa.

“Ko kafin na shiga siyasa, ina da ƙungiyar lafiya da ke bayar da magani da tiyata kyauta. Har yanzu aikin yana ci gaba, kuma yanzu na kammala gina babban asibiti a Azuba Fake da zai fara aiki a watan Satumba 2025,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce asibitin na dauke da na’urori na zamani, kuma za a rika bayar da magani kyauta da yardar Allah.

Har wa yau, Dr. Kigbu ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Gwamna Abdullahi Sule bisa amincewa da shi a matsayin wakilin jihar Nasarawa a hukumar ƙasa ta ƙidaya.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa yana da niyyar tsayawa takarar gwamnan jihar Nasarawa a shekarar 2027.

A nasa jawabin yayin karɓar aikin, Gwamna Abdullahi Sule, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Mohammed Sani-Bala, ya yabawa wannan aikin da ya bayyana a matsayin babbar gudummawa ga cigaban ilimi a jihar.

Advertisement

Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Dr. Aliyu Bello, ya taya Dr. Kigbu murna bisa kyautar da ya bayar, tare da kiraye-kirayen da ya yi ga sauran shugabanni da su rika tallafa wa jama’arsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending