News
Shugaban Kasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Fashewar Tayar Jirgin Sama
Shugaban ƙasar Laberiya, Joseph Nyuma Boakai, ya tsallake rijiya da baya bayan da jirgin sama da ya ke dauke da shi ya samu matsala a yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jiragen sama na Roberts International Airport (RIA), ranar Alhamis.
Rahotanni daga majiyoyi na kusa da filin jirgin sun bayyana cewa ɗaya daga cikin tayoyin jirgin ya fashe, lamarin da ya jefa cikin tashin hankali, inda fasinjoji da ma’aikatan jirgin suka shiga firgici. Jirgin na musamman ne mai saukar ungulu da ke jigilar manyan baki, wanda kuma ya dawo da Shugaba Boakai daga wata ziyara ta aiki da ya kai a Najeriya a farkon makon nan.
EFCC Ta Cafke Mutum Biyu Da Dala $899,800 Na Ƙudin Ɓogi A Kano
Bayan aukuwar lamarin, jami’an ceto na gaggawa da ke aiki a filin jirgin sun kai dauki cikin gaggawa, inda suka fitar da shugaban cikin koshin lafiya tare da rakashi zuwa cikin motarsa ta fadar shugaban ƙasa. Haka kuma, ƴan tawagarsa da ke cikin jirgin an fitar da su cikin kulawa ta musamman ta hanyar bus da ke cikin shirin agajin gaggawa na filin jirgin.
Wani babban jami’i a hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Laberiya ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara bincike kan musabbabin matsalar domin tabbatar da tsaron jiragen sama a nan gaba.
A sakamakon lamarin, wasu daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama da suka haɗa da Kenya Airways, Air Peace, da wasu da ke da shirin sauka a Monrovia a ranar, sun dakatar da ayyukansu har sai an tabbatar da cikakken tsaro a filin jirgin.
Sai dai, hukumar kula da filin jirgin RIA ta tabbatar cewa babu asarar rai ko rauni da aka samu, sannan kuma Shugaba Boakai da dukkan fasinjojin sun tsira lafiya.
