News
Kwamitin Zaman Lafiya Na Kano Ya Yi Kira Da A Yi Bukukuwan Sallah Cikin Natsuwa Da Zaman Lafiya
Kwamitin Zaman Lafiya na Jihar Kano ya taya Musulmi murnar bikin Babbar Sallah da za a fara gudanarwa daga ranar Juma’a, 6 ga Yuni, 2025.
Kwamitin ya bukaci al’ummar jihar da su gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
RANAR MUHALLI TA DUNIYA: Masana Sun Yi Kira Da A Dauki Mataki Kan Yawaitar Dattin Robobi A Kano
Wata sanarwa da kwamitin ya fitar a ranar Laraba, ta bukaci Musulmai da su yi koyi da Annabi Ibrahim (AS) ta fuskar hakuri, biyayya da sadaukarwa, wanda su ne ginshikin bikin Eid el-Kabir.
Shugabannin kwamitin, Dr. John Namaza Niyiring, OSA da Alhaji Aliyu Harazumi Umar (Dan Amar din Kano), sun ce lokaci ne da ya dace a kara rungumar juna da yi wa juna uzuri domin dorewar zaman lafiya a Kano.
“Zaman lafiya na bukatar hadin kan kowa da kowa. Ba aikin gwamnati ko jami’an tsaro kadai ba ne. Kowa na da rawar da zai taka,” inji kwamitin.
Kwamitin ya roki matasa da kada su bari a jefa su cikin fitina ko tada zaune tsaye, yana mai cewa: “Kada ku yarda wani ya yi amfani da ku wajen tayar da rikici.”
Ya kuma bukaci a yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin ci gaban Kano da Najeriya baki daya.
“Ina taya Musulmi murnar Babbar Sallah. Allah Ya maimaita mana cikin alheri da zaman lafiya,” inji kwamitin.
