News
Bello Turji Ya Ƙaƙaba Harajin Naira Miliyan 50 Kan Manoman Zamfara Da Neja
Shugaban ƴan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji, ya buƙaci manoma a wasu sassan Zamfara da Jihar Neja su biya harajin Naira miliyan 50 kafin su samu damar fara aikin gona a bana.
Wani masani kan harkokin tsaro, Bakatsine, ne ya bayyana hakan a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a da), yana mai nuna damuwa da yadda lamarin ke kara tabarbarewar tsaro da ci gaba a yankin.
‘Yan Bindiga Sunyi Ajalin Direbobi Biyu, Sun Ƙone Motocinsu A Imo
Rahotanni sun bayyana cewa Turji ya tura buƙatar biyan kudin daga mazauna yankin Tsalaken Gulbi a kauyen Fakai, cikin ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, har zuwa ƙauyen Qaya da ke kan iyakar Jihar Neja.
An dade ana danganta Turji da kai hare-hare, sace-sace da kuma karɓar kudin kariya daga manoma da mazauna karkara a jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.
Wasu daga cikin manoman da suka kasa biyan harajin na fuskantar barazana ga rayukansu da dukiyoyinsu, lamarin da ke kara jefa arewacin Najeriya cikin mummunar yunwa da tsananin talauci.
A cewar rahoton cibiyar bincike ta SBM Intelligence na shekarar 2024, manoma a fadin Najeriya sun biya fiye da Naira miliyan 139 ga ƴan bindiga tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023 domin samun damar yin noma cikin aminci.
