Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Gobarar Kasuwar Farm Centre 

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani kwamitin bincike na musamman da zai duba gobarar da ta tashi a kasuwar wayoyin salula ta GSM da ke Farm Centre, a birnin Kano.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya jagoranci kaddamarwar a madadin Gwamnan Kano, inda ya ce kwamitin zai binciki musabbabin gobarar da kuma yadda za a hana faruwar irin ta nan gaba.

Advertisement

Ya ce an nada kwamitin ne domin ya gano ainihin dalilan gobarar, ya tantance irin barnar da aka yi, da kuma bayar da shawarwari masu amfani da za su hana sake faruwar irin hakan.

Bello Turji Ya Ƙaƙaba Harajin Naira Miliyan 50 Kan Manoman Zamfara Da Neja

Ya kuma ja kunnen ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji siyasantar da batun tallafi ga wadanda gobarar ta shafa. Ya ce dukkan gudummawa da tallafi ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa za a rika karbarsu ta hannun kwamitin ko kuma ta asusun bankin da gwamnati ta ware domin hakan kamar yanda sanarwar Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Ciki Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar

Advertisement

ASUSUN TALLAFI:Sunan Asusun: FARM CENTRE GSM MARKET FIRE INCIDENCE SUPPORT FUNDS ACCOUNT, Lambar Asusun: 1310076187, Banki: ZENITH BANK

Shugaban Kwamitin shi ne Kwamishinan Aiyuka na  Musamman na Jihar Kano, Alhaji Nasiru Sule Garo, kuma kwamitin ya kunshi wakilai daga hukumomin gwamnati, na tsaro, kungiyoyin ‘yan kasuwa, da masu zaman kansu.

Advertisement

Wasu daga cikin hukumomin da ke cikin kwamitin sun hada da Ma’aikatar Tsaro da Ayyuka na Musamman, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Ciki, SEMA, Rundunar ‘Yan Sanda, DSS, KNUPDA, KACCIMA da kuma kungiyar ‘yan kasuwar GSM na Farm Centre.

Sauran sun hada da wakilan kananan hukumomi, manyan jami’an gwamnati da masu bayar da shawara, inda Alhaji Abdulkadir Shehu AGS-HOC zai kasance Sakataren kwamitin.

Advertisement

AYYUKAN KWAMITIN SUN HADA DA:

1. Binciken musabbabin gobarar.

Advertisement

2. Kimanta barnar da ta auku da asarar rayuka idan akwai.

3. Duba yadda hukumomi suka mayar da martani lokacin aukuwar gobarar.

Advertisement

4. Tantance matakan kariya da ke kasuwar a halin yanzu.

5. Bayar da shawarwari don hana aukuwar gobara a gaba.

Advertisement

6. Tattaunawa da wadanda abin ya shafa da sauran shaidu.

7. Tattara sunaye da bayanan wadanda suka yi asara.

Advertisement

8. Nazarin tsarin gine-ginen kasuwar da tsaron muhalli.

9. Samar da shawarwari kan yadda za a tafiyar da kasuwar cikin tsari.

Advertisement

10. Karbar duk wata gudummawa cikin sahihin asusun gwamnati.

11. Mikawa gwamnati cikakken rahoto cikin mako guda daga ranar da aka kaddamar da kwamitin.

Advertisement

Gwamnatin Kano ta ce tana daukar wannan lamarin da matukar muhimmanci kuma tana da niyyar sake gina kasuwar cikin tsari da kariya daga afkuwar gobara a gaba.

Ta kuma bukaci hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aikin kwamitin da kuma rage radadin da gobarar ta haifar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending