News
Ana Zargin Wata Uwa Da Ajalin ’Yarta Akan Naira 100 A Zariya
Wata mata mai suna Khadija tana fuskantar zargin kashe ’yarta mai suna Fadila, ’yar shekara 11, a unguwar Tukur Tukur da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Ana zargin matar da dukan Fadila da taɓarya har ta rasu, bayan da ta zarge ta da satar Naira 100 da ta samu a yawon Sallah.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, kuma ya tayar da hankali a yankin, inda wasu maƙwabta suka ce ba su yi wa yarinyar sallah ba saboda abinda suka ce rashin adalcin da aka yi mata.
Wasu maƙwabta sun ce wannan ba shi ne karon farko da Khadija ke dukanta ba.
“Idan ta tura ta talla aka samu matsala, sai ta lakada mata duka kamar ba yarta ba,” in ji wata matar unguwar.
Wani maƙwabcin ya ce, “Muka ƙi yi mata sallah saboda an zubar da gaskiya. An tafi da lamarin kamar ba komai ne ya faru ba.”
Mijin matar ya ce bai san abin da ya faru ba
A cewar mijin matar, Malam Mustapha Musa, lokacin da lamarin ya faru ba ya gida.
“Ina dawowa ne na tarar da abin. Ban san yadda aka yi abin ya faru ba,” in ji shi.
Ita kuma Khadija ta musanta zargin cewa ta kashe yarinyar.
“Na doke ta, amma ba da nufin kashe ta ba. Kuma a lokacin duk yaran gida ne kawai suke ciki,” in ji ta.
Gawar An Garzaya Da Ita Kano
Mahaifin Fadila ya ɗauki gawarta zuwa ƙauyensu da ke Jihar Kano domin yi mata sallah da binne ta.
Ya ce, “Na bar komai a hannun Allah.”
Hukuma na cikin bincike
Wani jami’in tsaron sa-kai ya ce sun gayyaci Khadija da mijinta ofishinsu domin su ba da bayani, amma daga baya suka janye bayan sun ga ’yan sanda sun iso wajen
Wakilinmu da ya kai ziyara ofishin ’yan sanda na Ɗan Magaji ya tarar da cewa babban jami’in ba ya nan, amma mataimakinsa ya ce ba su da cikakken bayani a kan lamarin.
Da aka tuntuɓi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya ce zai tuntuɓi ofishin yankin don jin halin da ake ciki.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu karin bayani daga ’yan sanda ba.
