News
Barrister Salisu Salisu Umar Ya Jajantawa ’Yan Kasuwar Waya Ta Farm Centre Kan Gobarar Da Ta Tashi
Fitaccen lauya kuma jigo a harkokin ci gaban al’umma, Barrister Salisu Salisu Umar, ya nuna alhini da jajantawa ga ’yan kasuwar waya ta Farm Centre da ke cikin birnin Kano, sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar, wadda ta yi sanadin asarar dukiyoyi da dama.
Ya bayyana hakan ne yayin zantawa da menama labarai a Kano a ranar labara, Barrister Salisu ya bayyana jin zafin lamarin, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya mayar wa masu hannu da shuni da abinda suka rasa, ya kuma kare aukuwar irin wannan ibtila’i a nan gaba.
Barrister Salisu ya yi kira ga gwamnati da shugabannin kasuwanni da su dauki matakin gaggawa na tabbatar da doka da tsarin amfani da na’urorin samar da wutar lantarki a kasuwanni. Ya ce wajibi ne a samar da ingantattun matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a guraren da ake yawan cudanya da kayan wutar lantarki da sauransu.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki matakin da ya dace wajen duba lafiyar tsarin tsaro a kasuwanni, da samar da horo da kayan aikin gaggawa ga masu kasuwanci, domin kaucewa irin wannan matsala ta nan gaba.
Ya ce, “Rayuka da dukiyoyin jama’a na da daraja a kowane lokaci, kuma wajibi ne a kare su da doka da tsari. Duk wata kasuwa na bukatar kulawa ta musamman domin ci gaba da habakar tattalin arzikin kasa.”
