News
Kano Online Media Chapel Ta Taya Makwarari Murnar Nadinsa A Matsayin Shugaban Himma FM Da Ke Kano.
Kungiyar ‘Yan Jarida na Kafafen Sadarwar Intanet a Jihar Kano (Kano Online Media Chapel) ta taya Isma’il Yusuf Makwarari murnar nadinsa a matsayin Manajan Tashar Himma Farmers 91.1 FM da ke Kano.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Abdulkadir Abubakar Dangambo, da sakataren kungiyar, Isiyaku Ahmed, suka fitar ranar Alhamis, kungiyar ta ce nadin ya dace da cancantar Makwarari.
Gwamnan Kano Ya Yabawa Hukumomin Agaji Bisa Dakile Yiwuwar Fashewar Tankar Mai A Titin Gwarzo
Sanarwar ta bayyana Makwarari a matsayin ɗan jarida mai kwazo, wanda ya ba da gudunmuwa sosai ga ci gaban kungiyar da aikin jarida gaba ɗaya.
“Ya nuna ƙwarewa da gaskiya a aikinsa. Ya kasance ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da suka tallafa wa ci gaban kungiyar tun farko,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta ce sabuwar rawar da Makwarari zai taka a tashar Himma Farmers za ta ƙara ɗora aikin jarida a jihar Kano a kan turbar da ta dace.
Ta kuma yi masa fatan nasara a sabon matsayin da aka ɗora masa.
