News
Wata Sabuwa: Malaman Jami’ar Yusuf Maitama Sule Sun Ƙi Amincewa Da Zaɓen Sabon VC

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano (YUMSUK), ta bayyana rashin amincewarta da yadda aka gudanar da zaɓen sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar (VC), inda ta bukaci a sauke Farfesa Ahmad Adamu daga matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na jami’ar.
A cikin wata wasika da ta aikawa Ministan Ilimi, kungiyar ta ASUU ta zargi Kwamitin Gudanarwar da keta ƙa’idoji da tsarin gudanar da zaɓen, tare da nuna damuwa kan ci gaba da riƙe Dr. Sadi Mohammed Sirajo a matsayin VC duk da cikar wa’adinsa na rikon kwarya.
Farfesa Gwarzo Ya Samu Lambar Girmamawa A Faransa – Wakiliyar UNESCO Ta Halarta
ASUU ta bayyana cewa an cire wakilan Majalisar Dattawa, Majalisar Malamai da Ƙungiyar Tsoffin Ɗalibai daga tsarin gudanar da zaɓen, wanda hakan ya sa zaɓen ya rasa inganci da sahihanci.
> “Duk wannan wasan kwaikwayon da ake yi, Kwamitin ne ke shirya shi don tilasta wanda suke so ya hau kujerar shugabanci. Hakan ya saba wa ƙa’idojin gudanar da jami’o’i,” in ji wata sanarwa daga ASUU.
Ƙungiyar ta kuma zargi Farfesa Ahmad Adamu da nuna fifiko da goyon baya ga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) a maimakon kare muradun YUMSUK, wanda hakan na iya haddasa rikici da rarrabuwa a cikin jami’ar.
Haka kuma, ASUU ta ce Dr. Sirajo ya ci gaba da riƙe muƙamin Shugaban Jami’ar ne ba bisa ƙa’ida ba bayan kammala wa’adinsa, tare da hana wasu malamai samun damar horo da ci gaba da aiki yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, rikicin na iya haifar da babbar matsala da tabarbarewar zaman lafiya da aikin gudanar da jami’ar.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga Kwamitin Gudanarwar Jami’ar ko daga shugabannin jami’ar ba dangane da ƙorafin ASUU.
ASUU ta bukaci Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da su sa baki cikin gaggawa domin dakile rikicin kafin ya ƙara kazancewa.