News
Mutane 7 Sun Gamu Da Ajalinsu A Harin Da Matasa Suka Kai Kan Motar Bas A Filato
Wasu matasa da ake kyautata zaton ‘yan yankin ne sun kai hari kan wata motar fasinja a karamar hukumar Mangu da ke Jihar Filato, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai tare da jikkatar wasu da dama.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:47 na dare, ranar Juma’a, 20 ga watan Yuni, 2025, a kusa da garin Mangu, inda motar bas din da ke dauke da fasinjoji 28 daga wata jiha makwabciya zuwa yankin Qua’an-Pan ta gamu da kwanton bauna.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa fasinjojin na kan hanyar zuwa wani daurin aure ne a yankin kafin lamarin ya afku.
Wani masani a harkar tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa, “A yayin da motar ke tsaka da tafiya cikin duhun dare, kwatsam wasu matasa suka tare ta, inda suka afka wa fasinjojin da muggan makamai, suka hallaka mutane bakwai a nan take, sannan suka banka wa motar wuta.”
Har ila yau, wani fasinja guda ya samu rauni mai tsanani, yayin da wasu shida suka jikkata.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa an samu nasarar ceto mutane 14 da ba su samu rauni ba, sakamakon saurin daukar mataki da wasu shugabannin yankin suka yi.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Mangu domin samun kulawar gaggawa, yayin da hukumomin tsaro suka tura tawagar jami’ai zuwa yankin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike da kuma kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Ko da yake har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu wata sanarwa kai tsaye daga rundunar ‘yan sandan jihar Filato ko sojoji ba, amma majiya daga bangaren tsaro ta tabbatar da cewa an fara daukar matakai domin tabbatar da doka da oda a yankin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
