News
Gwamnan Kano Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Kano 2 A Benue
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da wasu suka yi wa Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad a Makurdi, jihar Benue.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Gwamnatin Adamawa Ta Kwace Sarautar Wazirin Adamawa Daga Hannun Atiku
BBC HAUSA ta ruwaito cewa An kai wa matasan hari ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a wani yanki na Makurdi, inda aka kashe su.
Gwamna Abba ya bayyana mutuwar a matsayin ta’asa, yana mai jaddada cewa gwamnati tana aiki tare da hukumomin tsaro da gwamnatin Benue domin tabbatar da cewa an cafke masu hannu a lamarin.
Ya ƙara da cewa kowane ɗan Najeriya na da ’yancin zama da rayuwa a kowace jiha ba tare da barazana ba, kuma Kano za ta ci gaba da kare ’yan asalinta a ko ina suke.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
