News
Gwamnatin Adamawa Ta Kwace Sarautar Wazirin Adamawa Daga Hannun Atiku
Gwamnatin Jihar Adamawa ta sanar da warware sarautar gargajiya ta Wazirin Adamawa da ke hannun tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, bisa dalilan da suka shafi daidaiton tsarin sarautun gargajiya a fadin jihar.
A wata takarda da ta fito daga Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, mai dauke da kwanan wata 20 ga Yuni, 2025, wacce Sakatariyar Sashen Kula da Sarautu, Misis Adama Felicity Mamman ta sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa duk wani mai rike da sarauta a cikin majalisun sarautu a jihar, ya zama wajibi ya kasance dan asalin yankin da masarautar ta fito.
Yadda Ƴan Najeriya Za Su Nemi Aikin NSCDC, NIS, NCoS Da FFS
A cewar sanarwar ta ce “Bayan nada sabbin Sarakunan Gargajiya da Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri ya amince da su, an umurce ni da in shaida cewa dukkan masu rike da sarautun hakimi da na majalisar sarauta a jihar, dole ne su kasance ‘yan asalin masarautunsu.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Misali, masu rike da sarauta a Majalisar Masarautar Adamawa dole ne su kasance ’yan asalin Yola ta Arewa, Yola taKudu, Girei, Mayo
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
