News
Yadda Ƴan Najeriya Za Su Nemi Aikin NSCDC, NIS, NCoS Da FFS
Gwamnatin tarayya ta sanar da ɗaukar ma’aikata 30,000 a hukumomin Immigration, Civil Defence, Correctional da Fire Service a faɗin ƙasar.
Kwamitin CDCFIB ya ce ɗaukar aikin zai haɗa da guraben aiki a Hukumar Kula da Shige da Fice, Hukumar Gidajen Gyaran Hali, Hukumar Kashe Gobara da NSCDC.
Za a buɗe ƙofar neman aiki ranar 26 ga Yuni a shafin: recruitment.cdcfib.org.
Masu nema dole ne su zama ‘yan Najeriya masu shekaru 18 zuwa 35 da cika ƙa’idojin lafiyar jiki da ta hankali.
Maza su kai tsayin 1.65m da faɗin ƙirji 0.87m; mata kuwa su kai aƙalla 1.60m.
Dole ne masu nema su zama masu kyakkyawan hali, ba tare da tarihin laifi ba.
Ana buƙatar takardar kammala sakandare tare da nasarar cin aƙalla darussa huɗu ko biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Masu NCE, OND, HND, digiri ko takardun sana’a a fannonin fasaha suma ana ƙarfafa musu gwiwa su nema, The Cable ta ruwaito.
An gargaɗi masu nema da su tsaya a hukuma guda ɗaya kawai, domin neman gurabe fiye da ɗaya zai janyo ƙin amincewa.
Ana sa ran rufewar shafin neman aikin cikin makonni uku bayan buɗe ƙofar neman aikin.
