Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirin Magance Matsalar Karancin Ruwan Sha

Published

on

Yan ga ruwa

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na shawo kan matsalar karancin ruwan sha da ke addabar wasu yankunan jihar.

Kwamishinan Ruwa na Jihar Kano, Alhaji Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan a lokacin wata ziyarar duba aikin da ya kai a matatar ruwan Joda, da ke Karamar Hukumar Gabasawa.

Gwamnan Kano Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Kano 2 A Benue

A cewar Kwamishinan, gwamnati ta samar da sabon injin tura ruwa daga madatsar zuwa kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa, da kuma wasu sassan unguwannin Nasarawa da ‘Yan Kaba.

Doguwa ya ce wannan mataki wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da wadataccen ruwan sha ga al’ummar da abin ya shafa.

“Hukumar samar da ruwa a jihar tana ci gaba da gyare-gyare a sauran matatun ruwa domin kara inganta rabon ruwa ga jama’a,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma tabbatar wa da mazauna yankunan da suka fi fuskantar matsalar cewa nan bada jimawa ba za su fara jin sauyi wajen samun ruwan sha mai tsafta.

Advertisement

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Yankin Gezawa, Jamilu Mustapha Yakasai, a ranar Talata.

Doguwa ya ce gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na daukar wannan aiki da matukar muhimmanci domin saukaka wa jama’a rayuwa da kuma inganta lafiyar su.

 

PREMIER RADIO 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending