Connect with us

News

Kwankwaso ya ci amanarmu, Mun bar wa APC shi – NNPP

Published

on

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana cewa ba ta da wata damuwa idan tsohon dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Oginni Olaposi, ya fitar a ranar Lahadi a Legas, biyo bayan murabus din tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma rade-radin cewa murabus din Ganduje na da nasaba da shirin shigo da Kwankwaso cikin APC.

Advertisement

Yara 150,000 Ke Haifuwa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto

Olaposi ya zargi Kwankwaso da cin amanar jam’iyyar NNPP, yana mai cewa Kwankwaso ya yi kokarin kwace jam’iyyar daga hannun wanda ya kafa ta, Dokta Boniface Aniebonam, bayan samun damar takarar shugaban kasa a kyauta a shekarar 2023.

“Kwankwaso ya ci amanar da muka ba shi ta hanyar kokarin kwace jam’iyyar daga hannun wanda ya kafa ta, Dokta Boniface Aniebonam, wanda ya ba shi tikitin takarar shugaban kasa a 2023 ba tare da wani sharadi ba,” in ji Olaposi.

Advertisement

Ya ce a yanzu babu wata baraka a zuciyar NNPP dangane da makomar Kwankwaso.

“Idan ya koma APC, zai fi mana dadi. Ya nuna tun da farko cewa bai da kishin NNPP. Mun sallame shi tun tuni,” in ji shi.

Advertisement

Olaposi ya kara da cewa NNPP na ci gaba da gyara tsarinta domin sake gina martabarta a fagen siyasar Najeriya, tare da jajircewa wajen kare muradun dimokuradiyya da ci gaban kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending