News
Yara 150,000 Ke Haifuwa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto
Rahotanni daga kwararru a fannin lafiya sun bayyana cewa, a kalla yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a Nijeriya a duk shekara, lamarin da ke kara tayar da hankali kan matsalolin da ke tattare da rashin ingantattun gwaje-gwaje da kuma rashin isasshen wayar da kan al’umma.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fitar a yayin bikin ranar wayar da kai game da cutar Sikila ta duniya, Mataimakin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ma’aikatar, Mista Alaba Balogun, ya bayyana cewa kashi 25 cikin 100 na magidanta a Nijeriya na dauke da kwayar cutar.
Ya ce, “A duk shekara ana samun haihuwar kusan jarirai 150,000 da ke dauke da cutar Sikila, lamarin da ke da nasaba da kashi 8 cikin 100 na mace-macen jarirai a kasar.”
Tasirin Cutar Ga Lafiyar Jama’a
Balogun ya kara da cewa, wadanda ke rayuwa da cutar na fuskantar kalubale iri daban-daban, ciki har da lalacewar gabobin jiki, shanye jiki, kamuwa da wasu cututtuka masu tsanani, da kuma matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa.
A cewarsa, cutar Sikila na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ke barazana ga cigaban ilimi, aikin yi da walwalar rayuwar jama’a, musamman a tsakanin matasa.
Matsalar Rashin Ingantattun Gwaje-Gwaje
Wani babban matsala da masana suka bayyana shi ne, yawaitar sakamakon gwaji na bogi daga dakunan gwaje-gwaje da ba su da inganci.
Dakta Ifeanyi, wani kwararre a fannin dakunan gwaje-gwaje, ya ce, “Yawaitar cibiyoyi da dakunan gwaje-gwaje na bogi da ma’aikatan da ba su da cancanta, na daya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa yaduwar cutar Sikila a tsakanin ma’aurata.”
Ya bayyana cewa, “An samu karuwar ma’aurata da ke haihuwar yara masu dauke da cutar, sakamakon sakamakon gwaji na karya da aka basu kafin su yi aure.”
Kwarewar Iyaye Kan Matsalar
Wata uwa daga unguwar Dagbana a Abuja ta bayyana wa LEADERSHIP cewa, sun samu sakamakon gwaji mara kyau kafin aure wanda ya janyo musu haihuwar ‘ya’ya masu cutar.
“Mun yi gwajin da ake bukata kafin aure, aka ce ni AA ce, mijina AS, sai dai daga baya aka gano cewa yarona SS ne,” in ji ta cikin alhini.
Ita ma wata mata daga Nyanya, Madam Mary Ukaibe, ta bayyana irin irin kuskuren da aka yi mata, inda aka fada mata cewa AA ce, amma daga baya aka gano AS ce ita.
Kiran Gaggawa Ga Hukuma
Dakta Ifeanyi ya bukaci hukumar MLSCN da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, su dauki mataki na gaggawa wajen magance wannan matsala.
Ya ce, “Dole ne a sanya ido sosai kan dakunan gwaje-gwaje, tare da tabbatar da cewa dukkan kayayyakin gwaji da ma’aikatan da ke yin gwajin sun cancanta.”
Haka zalika, ya bukaci kungiyoyin addini, sarakunan gargajiya da kungiyoyin farar hula da su kara zage damtse wajen wayar da kan jama’a game da cutar da kuma illar auren da ba a yi gwaji mai inganci ba kafin shi.
Matakin Gwamnati Kan Yaki Da Cutar
Mataimakin Daraktan Sashen Gwaje-gwaje na Babban Asibitin Tarayya da ke Abuja, Anthony Ilegogie, ya gargadi ‘yan Nijeriya da su guji dogaro da dakunan gwaje-gwajen da ba su da inganci.
Ya ce, “Yanayin halittar mutum ba ya canzawa. Bayan an yi gwaji na gaskiya, bai kamata a sake komawa a ce za a sake gwaji ba.”
A cewarsa, sababbin na’urorin zamani na bayar da sahihin sakamako idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.
Nijeriya Na Kan Gaba A Duniya
Rahotannin LEADERSHIP sun nuna cewa, Nijeriya na daga cikin kasashe da suka fi fama da cutar Sikila a duniya, inda kashi 25 cikin 100 na manya ke dauke da kwayar cutar, yayin da yara kimanin 150,000 ke kamuwa da ita a duk shekara.
Farfesa Obiageli Nnodu, Mashawarcin Musamman Kan Cutar Sikila ga Ministan Lafiya, ta bayyana cewa, a halin yanzu sama da mutane miliyan hudu ne ke rayuwa da cutar Sikila a fadin kasar.
A karshe, masana sun jaddada bukatar hada karfi da karfe wajen yaki da cutar, ta hanyar wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin gwaje-gwaje a fadin kasar.
