News
Yadda Wani Manomi Ya Ceci Jaririyar Da Aka Binne A Gonarsa Bayan An Haife Ta
Wani manomi mai suna Malam Kabiru Kamba daga garin Kamba, karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi, ya ceto wata jaririya mace da aka binne a gonarsa bayan an haife ta.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a lokacin da Kabiru ya lura da wani tudu daban a cikin gonarsa wanda bai saba gani ba.
Saboda shakku, sai ya nemi taimakon wasu mahaya babura su taimaka masa wajen tono wurin, inda suka gano jaririyar.
Bayan haka, Kabiru ya sanar da ‘yan sanda dake kusa da wurin, wadanda suka zo suka ci gaba da tono wurin har suka tabbatar da cewa jaririn na nan cikin koshin lafiya.
Daga nan ne aka mika jaririyar ga Kabiru domin ya kula da ita har sai an kammala bincike.
Matar Kabiru ta nuna farin ciki da kuma shirin kula da jaririyar kamar ta ta, tana mai cewa za ta yi duk mai yiwuwa domin ta samu kulawa.
A lokaci guda, wata tawagar kungiyar da ke yaki da cin zarafin mata da yara ta jihar Kebbi, wadda Hajiya Rafa’atu Hammani ta jagoranta, ta ziyarci Kabiru domin nuna godiya da goyon baya.
Sun kuma tabbatar da cewa za su kai rahoton wannan lamari ga Uwargidan Gwamnan jihar, Hajiya Zainab Nasare Idris, domin samun karin tallafi.
Tawagar ta kuma yaba wa ‘yan sandan Najeriya saboda saurin daukar mataki wajen bincike da kokarin gano wanda ya aikata wannan mummunar aiki.
Sun kuma bayar da tallafi ga jaririyar ta hanyar kawo kayan bukatu kamar sutura, sabulu, diapers, gado, madarar jarirai, da sauran kayan taimako.
