Connect with us

Politics

An naɗa David Mark da Aregbesola a matsayin shugaba da shakaren riƙon ƙwarya a ADC

Published

on

1751398127754

A wani yunƙuri na samar da tafiyar da za ta kawo ƙarshen mulkin Shugaba Bola Tinubu a 2027, ƴan ɓangaren adawa a jam’iyyar ADC, sun naɗa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakatare na riƙon ƙwarya a jam’iyyar.

Muryoyi da dama bayan kammala zaman ƴan jam’iyyar a daren ranar Talata wayewar Laraba sun shaida cewa, jagorancin jam’iyyar ya amince da naɗin mutane biyun.

Advertisement

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Jita-jitar Saka Dokar Hana Fita A Wasu Yankunan Birnin

Haka kuma, muryoyin, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu kasancewar ba a ba su izinin bayyana hakan ba a hukumance, sun ce an kuma zaɓi tsohon ministan wasanni, Bolaji Abdullahi a matsayin sakataren yaɗa labarai.

Sun ƙara da cewa, a yau Laraba ne za a ƙaddamar da jam’iyyar da shugabancinta a hukumance, a Abuja.

Advertisement

Kasancewar gwamnatin Shugaba Tinubu tana fama da matsalolin koma-baya a ɓangarori da dama na jagorancin ƙasar, hakan ya sa ta ke samun suka daga ɓangaren ƴan adawa da jam’iyyu da dama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending