Politics
Muna Yi Wa Masu Shigo Wa ADC Maraba, Amma Ba Za Mu Bari A Ture Kaza A Kwashe Kwai Ba —Malam Ibrahim Khalil
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓen 2023, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa jam’iyyar su na maraba da sababbin mambobin da suka shigo daga wasu jam’iyyu, musamman masu haɗakar siyasa da suka sauya sheƙa zuwa ADC.
Malam Khalil ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan sauya sheƙar wasu ’yan adawa zuwa jam’iyyarsu, inda ya bayyana hakan a matsayin ci gaba ga dimokuraɗiyyar Najeriya kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito.
Kotu Ta Tura Matashi Gidan Gyaran Hali Bisa Zargin Jagorantar ‘Yan Daba A Kano
Sai dai, ya bayyana cewa duk da maraba da suke yi da sababbin mambobi, hakan ba zai hana su kare haƙƙin tsoffin mambobi ba.
“Mun karɓi sababbin mambobi da hannu bibbiyu, amma mu a ADC ba za mu bari a ture kaza a kwashe kwai ba. Kowa ya san matsayinsa, mu yi siyasa da adalci da mutunta juna,” inji Malamin.
Ya ce ADC jam’iyya ce da ke bin tsarin siyasa na gaskiya da adalci, kuma tana da buƙatar hadin kai da mutunta juna domin cimma manufofin da ta sa a gaba.
Malamin ya ƙara da cewa, “Siyasa ba ta daɗi idan aka fara danniya da son zuciya. Idan muna so mu yi canji na gari, dole ne mu mutunta juna.”
Jawabin Malam Khalil na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karbar sababbin mambobi daga wasu jam’iyyu zuwa ADC, lamarin da ke nuna yadda faɗin siyasa ke ƙara canzawa a Najeriya, musamman a shiyyoyin da ke fama da rikice-rikicen jam’iyyu.
