News
Farfesa Gwarzo ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sanya wa wata jami’a sunan marigayi Aminu Ɗantata
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, mamallakin rukunin jami’o’I na MAAUN ya roƙi gwamnatin tarayya da ta karrama marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata ta hayar sanya sunansa a ɗaya daga cikin jami’o’in da ke yankin Arewa maso yamma.
Farfesa Gwarzo ya yi wannan roƙo ne a ranar Laraba inda ya ce mutanen yankin za su yi farin ciki da hakan saboda irin gagarumar gudunmowar da ya bayar a ɓangaren ilimi a lokacin rayuwarsa.
“Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta karrama marigayi Alhaji Aminu Dantata ta hanyar sanya sunansa a ɗaya daga cikin jami’o’i da ake da su saboda irin gudunmowar da ya bayar a ɓangaren ilimi,” farfesa Gwarzo.
Ambaliya A Mokwa: ‘Yan Majalisa Sun Ce Mutane 600 Da Suka Ɓace Ba Sa Raye
Ya ce ta wannan hanyar wannan ne za a tuna da irin gudunmowar da ya bayar a ɓangaren ilimi domin a riƙa tunawa da shi da kuma zama abin kwaikwayo ga ‘yan baya.
“Ɗantata ya zuba jari a ɓangaren ilimi – ya ba da tallafi da gine-gine ga makarantu ta hanyar Gidauniyar Dantata da sauran shirye-shiye.
Sannan ya ba da tallafin karatu ga ɗalibai marasa ƙarfi, ga shi mutum na farko da ya zama shugaban jami’ar Al-Qalam da ke Katsina,” ya bayyana.
Gwarzo wanda shi ma ya yi fice a harkokin ilimi, ya bayyana Ɗantata da mutum mai taimaka wa al’umma kuma jagora wanda za a cigaba da mararinsa saboda gagarumar gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da yankin yammacin Afirka.
Don haka sanya wa wata jami’a sunansa zai faranta wa al’umma musamman wadanda suka ci gajiyar ayyukansa na alheri a cewar Farfesa Gwarzo
